Ana son Charles Taylor ya shekara 80 a kurkuku

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Charles Taylor

Masu shigar da kara a shari'ar tsohon shugaban kasar Liberia, Charles Taylor, sun bukaci a yanke masa hukuncin zaman kaso na shekaru tamanin, bayan samunsa da aka yi da aikata laifukan yaki a makon jiya.

A wata rubutacciyyar bukata da suka shigar a gaban Kotun Musamman mai Hukunta Laifukan Yakin Saliyo, masu shigar da karar sun ce wannan hukuncin ne zai yi daidai da girman laifuffukan Mista Taylor.

Kotun, mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, ta samu Mista Taylor ne da laifin goya baya ga wata kungiyar 'yan tawaye wacce ta yi kaurin suna wajen kisa, da aikata fyade da kuma guntule gabobin jama'a yayin yakin basasar shekaru goma sha daya a kasar ta Saliyo.

A ranar talatin ga watan Mayu dai za a yanke masa hukunci.

Karin bayani