Khalid Sheikh Mohammed a gaban kotu

Khalid Sheik Muhammed
Image caption Khalid Sheik Muhammed

Mutumin nan da ake zargi da kitsa harin ranar 11 ga watan Satumban 2001 da aka kaiwa Amurka, ya gurfana a gaban kotun soja a sansanin Guantanamo.

Sai dai Khalid Sheikh Muhammed ya ki maida martani ga tambayoyin da ake yi masa a kotun sojan.

Lauyansa ya ce, ya ki saurarorin kalaman alkalin kotun ne, saboda rashin amincewa da azabtar da shi da aka yi.

Wannan dai shi ne yunkuri na biyu domin gurfanar da Khalid Sheik Muhammed a gidan yarin na Guantanamo Bay.

A shekara ta 2008 ya gurfana a gaban wannan kotu, inda ya ce shi ya shirya harin na ranar 11ga watan Satumban, kuma ya ce zai amsa laifin.

Sai dai lauyoyin da ke kare shi sun ce, kotun, wadda ta soja ce, ba ta da halacci.

Karin bayani