An kashe mutane biyar a Taraba

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan sandan Najeriya

A jihar Taraba da ke arewacin Najeriya, ranar Juma'a ne wasu mutane sanye da kayan soji suka bi gida-gida inda suka kama mutane bakwai, suka kai su daji, kana suka harbe biyar daga cikinsu har lahira.

Lamarin dai ya auku ne a garin Dan Anacha, kusa da inda aka kama Kabiru Sokoto, mutumin da hukumomin Najeriya ke zargi da dana bom a wata majami'a ranar Kirsimetin da ta wuce.

Hukumomin tsaro dai sun ce mutanen da suka yi kisan ba ma'aikatansu ba ne.

Batun ya sanya hankulan mutanen garin sun tashi inda ake ci gaba da zaman dar-dar.

Ko a ranar Litinin din da ta gabata ma dai sai da wani dan kunar-bakin-wake ya kaiwa tawagar kwamishinan 'yan sandan jihar hari, al'amarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Karin bayani