An hallaka 'yan bindiga a Kano

Kano a taswirar Najeriya Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Kano a taswirar Najeriya

Rundunar tsaro ta hadin gwiwa a jihar Kano, JTF, ta ce jami'anta sun kashe 'yan bindiga hudu, sun kuma kama wasu, a wani samame da suka kai yau a unguwar Kwari, a yankin Hotoro dake gabashin birnin.

Rahotanni daga yankin sun ce, an yi ta jin karar harbe-harbe har tsawon fiye da sa'a guda.

Al'amurra sun tsaya cik a unguwar, sakamakon harbe harben.

A 'yan watannin nan jahar ta Kano ta yi fama da hare haren da ake dangantawa da kungiyar Boko Haram.

Daruruwan jama'a - fararen hula da jami'an tsaro - ne suka rasa rayukansu.

Karin bayani