Amurka ta wargaza shirin hari a jirginta

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Barrack Obama

Jami'ai a kasar Amurka sun ce, su, da kawayensu sun wargaza wani shiri da aka yi na tarwatsa wani jirgin saman Amurka ta hanyar amfani da wata na'ura.

Na'urar dai irin wadda aka gaza samun nasara da ita ce lokacin da dan Najeriyan nan Umar Mutallab ya sa bam a dan kanfai ya nemi tarwatsa wani jirgin saman da ya ta so daga yemen zuwa Amurka a shekara ta dubu biyu da tara.

Jami'an suka ce wata kungiya ce mai alaka da kungiyar Al-Qaeda ta shirya makarkashiyar harin na kunar bakin-waken, an kuma yi shirin ne ya zo daidai da lokacin cika shekara daya da rasuwar Osama bin Ladan.

A yanzu wannan na'ura tana hannun hukumar bincike ta FBI.

Karin bayani