Faransa: Hollande yana tattaunawa da shugabannin duniya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Francois Hollande

A Faransa, zababben shugaban kasa dan gurguzu Fracois Hollande yana cigaba da zantawa da shugabanni da da ma na kasashen duniya, yana kuma shirin kama ragamar ikon mulki.

A lokacin yakin neman zabensa na Shugaban kasa, ya yi kiran da a sabunta bayar da fifiko a cikin kungiyar Tarayyar Turai a kan karfafa habbakar tattalin arziki a matsayin wata hanya ta kawar da matsalar bashi da rashin ayyukan yi.

Wakilin BBC a birnin Paris ya ce akwai yiwuwar bullo da wani shiri wanda zai iya hadawa da yarjejeniya a kan habbakar tattalin arzikin da za ta jera kafada-da-kafada da yarjeniyar da ake aiki da ita a yanzu.

Karin bayani