Merkel ta ce yarjejeniyar Turai tana nan

markel Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Merkel da Franois Hollande

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce yarjejeniyar da aka cinma ta tarayyar Turai kan tsara kudade, ba wata ce wadda za a nazari kan ta ba, duk da kiran da shugaban Faransa mai jiran gado, Francois Holande ya yi na a yi hakan.

Misis Merkel ta ce nan a Jamus, ra'ayinmu shi ne, kuma ni ma na yi imanin cewa babu batun sauya yarjejeniyar tsuke bakin aljihun.

Kasashe ashirin ne suka tatuna suka rattaba hannu a kanta.

Ta kuma ce yana da muhimmanci kasar Girka ta tsaya kan shirye shiryen da aka amince da su na kawo gyara a tsarin tattalin arziki, wanda a dalilinsa kungiyar tarayyar turai da hukumar bada lamuni ta duniya IMF suka amince su ba ta wasu kudade na ceto tattalin arzikin kasar.

Karin bayani