Jam'iyyun da ke adawa da tsuke bakin aljihu sun yi nasara a Girka

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Daya daga cikin 'yan majalisar dokokin da suka lashe zabe a Girka

A babban zaben da aka gudanar a Girka, akasarin jama'a sun kada kuri'unsu ne ga jam'iyyun da ke adawa da matakan tsuke bakin aljihun da kasar ke fama da su.

Su kuwa manyan jam'iyyun kasar masu goyon bayan matakan, wadanda aka dauka don samun tallafi daga cibiyoyin kudi na duniya, kusan sulusin kuri'un kacal suka samu.

Daya daga cikin jam'iyyun biyu, New Democracy, ita ta fi yawan wakilai a majalisar, kuma doka ta debawa shugabanta, Antonis Samaras, kwanaki uku ya kafa gwamnatin gamin gambiza.

A cewarsa, ''A shirye muke mu dauki alhakin kafa gwamnatin ceto kasa mai manufofi guda biyu: kasar ta ci gaba da kasancewa cikin kasashe masu amfani da kudin euro, sannan kuma a yi garambawul a yarjejeniyar karbo tallafi ta yadda al'ummar Girka za ta samu sa'ida''.

Karin bayani