BBC navigation

Hollande na yunkurin kafa sabuwar gwamnati

An sabunta: 7 ga Mayu, 2012 - An wallafa a 07:12 GMT

Francois Hollande

A ranar Litinin ne sabon shugaban kasar Faransa, Francois Hollande, zai fara yunkurin kafa sabuwar gwamnati bayan nasarar da ya samu a zaben shugaban kasar.

An kwana ana shagulgula a Paris, inda Mista Hollande ya shaidawa magoya bayansa, wadanda akasarinsu masu ra'ayin gurguzu ne, cewa nasararsa za ta kawo kyakkyawan fatan ganin bayan matakan tsuke bakin aljihu ga daukacin al'ummar Turai:

''Ku isar da wannan sako ko'ina. Ku rika tuna wannan gagarumin taro na dandalin Place de la Bastille iya tsawon rayuwarku domin zai isar da sakon sauyin da muka kawo yanzu ga sauran al'ummar Turai''.

Merkel ta nemi tattaunawa da Hollande

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, wacce ta marawa Nicolas Sarkozy baya a zaben na Faransa, ta taya Mista Hollande murnar nasarar da ya yi, ta kuma gayyace shi wata tattaunawa a Berlin.

Ministanta na harkokin waje, Guido Westerwelle, ya ce yana da kwarin gwiwa kasashen biyu za su yi aiki tare don samar da yarjejeniyar ci gaban tattalin arziki ga kasashe masu amfani da kuidn euro.

A cewarsa, ''Wannan sakamako ne mai dimbin tarihi aka samu a Faransa; zan so in karfafa cewa muna da aniyar yin aiki tare da sabon shugaban kasar Faransa''.

Sai dai kuma Misis Merkel ta ce bakin alkalami ya riga ya bushe dangane da batun sauyi a manufar Tarayyar Turai ta tsuke bakin aljihu.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.