Ana zaman dar dar a Potikusm

potiskum
Image caption Taswirar Najeriya dauke da Potiskum

A Najeriya rahotanni daga garin Potiskum a jihar Yobe arewacin kasar sun ce jama'a da dama ne suke tsere daga gidajen su yayinda kasuwanni da shaguna suka kasance a rufe sakamakon wata tarzoma da ta barke.

Rikicin ya fara ne bayan da wasu gungun matasa suka fara kone kone, su kuma jami'an tsaro suka fara mayar da martani da harbe harbe domin tarwatsa su.

Hakan na faruwa ne jim kadan bayan wani taron addu'oi da dubun dubatar 'yan kasuwa , da malamai da wasu mutanen garin suka gudanar, a harabar bakin kasuwar shanu.

Kasuwar da a makon da ya gabata, wasu 'yan bindiga suka kai harin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane sama da talatin, tare da jikkata wasu da dama.

Karin bayani