An kori likitoci dari takwas a jihar Lagos

Wani asibiti a Najeriya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wani asibiti a Najeriya

A Nijeriya, gwamnatin jihar Lagos ta kori likitoci kusan dari takwas , bayan da suka shiga wani yajin aiki na sai abin da hali ya yi.

A sakamakon haka, ma'aikatan jiya ne kawai ke kula da marasa lafiya a asibitoci, amma gwamnatin jihar ta ce tuni ta dauki wasu sabbin likitocin fiye da dari uku.

Rahotanni na cewa marasa lafiya da dama sun mutu a sakamakon yajin aikin da likitocin ke yi wadanda ke son gwamnatin ta kyautata albashinsu.

Kungiyar Likitocin jihar ta Lagos dai ta bayyana matakin gwamnatin jihar da cewa ba ya kan ka'ida, kuma ta yi barazanar kai maganar gaban kotu.