Ana dauki ba dadi a Tripoli babban birnin Libya

Abdel-Rahim al-Kib Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Abdel-Rahim al-Kib

Ana can ana bata kashi kusa da ofishin Firayi Ministan Libya dake birnin Tripoli.

Wasu tsaffin 'yan tawaye ne suka kai hari saboda an ki biyan su albashi.

Kakakin Firayi Ministan ya shaidawa BBC cewar an kashe mutane biyu kuma ana ta musayar wuta a cikin ginin.

A halin yanzu dai, akwai manyan motacin goma da makamai sun zagaye harabar ginin.

Kawo yanzu dai babu wanda ya san inda Firayi Minista yake.

Karin bayani