An kai hari a ofishin Fryministan Libya

Abdel-Rahim al-Kib Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Abdel-Rahim al-Kib

An kai hari da makamai a kan ofishin Fryministan Libya a birnin Tripoli.

An kyautata zaton tsoffin 'yan tawaye ne suka kai hare haren,yayinda suke neman a biya su albashinsu.

An bada rahotanin kashe mutane biyu.

Wani mashawarcin Fryminstan ya ce hare-haren ba su taba lafiyarsa ba.

A yanzu an ce jami'an tsaro dake goyon bayan gwamnati ne ke gadin ginin.

Karin bayani