Kofi Annan ya yi gargadi akan Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters

Wakilin musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Syria, Kofi Annan ya yi gargadin cewa shirin samar da zaman lafiya a kasar shine kadai mafita don kaucewa fadawa yakin basasa a Syriyar.

A cewar sa akwai babbar matsala idan har aka kasa shawokan batun.

Mista Annan ya bayyana haka ne, jim kadan bayanda ya gabatarwa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya jawabi akan yanayin da ake ciki a Syria.

Har yanzu dai, ana cigaba da tashin hankali tsakanin sojoji da 'yan adawa duk da cewar an tura masu sa'ido na majalisar dinkin duniya a kasar.

Karin bayani