Shugabannin Afrika na tattaunawa kan tattalin arziki

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jean Ping

Shugabannin kasashen Afrika da manyan 'yan kasuwa na kasashen waje suna ga nawa a birnin Addis Ababa na Ethiopia don tattauna hanyoyin da za a bunkasa cigaba da zuba jari a nahiyar.

Taron bunkasa tattalin arzikin Afrikar na duniya na kwanaki uku zai maida hankali ne a kan batutuwa na kirkirar guraben ayyukan yi da kyakkyawan shugabanci da kyautatuwar muhalli.

Masu shirya taron sun ce nahiyar Afrika wurinda ake da kasashe goma da tattalin arzikinsu ke habaka cikin hanzari - tana dab da samun manyan sauye-sauyen tattalin arziki.

Sai dai wasu kasashen Afrika na fama da matsalolin rashin tsaro da rikice rikicen shugabanci da safarar kwayoyi da makamai.

Karin bayani