Ta'addanci: Dan Burtaniya ya gurfana a kotu a Kenya

Wani Dan Birtaniya da ake zargi da kaifin kishin Islama ya bayyana a gaban wata kotu a Birnin Mombasa na gabar ruwan Kenya.

An kama Jermaine Grant mai shekaru 29 ne a watan Disamba, kuma ya musanta zargin cewar yana shirin kai wani harin bam da kuma mallakar wasu ababuwan da ka iya fashewa.

Dan London din wanda hukumomin Kenya suka ce yana da alaka da yan gwagwarmayar Somalia na Al-Shabaab, tuni an tsare shi saboda kasancewa a kasar ba bisa ka'ida ba.

An dai daga shara'ar har ya zuwa ranar gobe, a yayinda ake hatsaniya a kotun.

Wani rahoto da cibiyar kwararru ta Royal United Services dake Burtaniya ta fitar ya nuna cewa akwai kimanin 'yan asalin Burtaniya 50 cikin 'yan wasu kasasshen waje 200 dake yaki tare da 'yan kungiyar Al Shabaab.

Tun da farko dai an tsare Mr Grant din ne a Kenya kusa da kan iyakar Somalia a shekarar 2008, sai dai wasu da ake zargin cewa 'yan kungiyar Al -shabaab sun kubutar da shi daga hannun jami'an sanda.