Kofi Annan ya yi kashedi kan Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption masu sa ido a Syria

Wakilin musamman na Majalisar dinkin duniya, Kofi Annan ya yi kashedin cewa shirin zaman lafiya na Syria da ake aiki da shi a yanzu, zai iya zama da ma ta karshe da za ta kawar da afkuwar ya kin basasa a kasar.

To, amma Prime Ministan Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce, shi gwiwoyinsa sunyi sanyi ga yiwuwar nasarar shirin.

Mr Erdogan yace lallai ne a tura ka rin wakilan Majalisar dinkin duniya masu sa ido har zuwa dubu ukku don kauce wa afkuwar cikakken ya ki.

Mr Annan dai yana sa ran zuwa karshen watan nan ne za a tura sauran masu sa idon da za su kai adadin dari uku a Syriar.

A cikin kasar ta Syria ana cigaba da tashin hankali, a ranar talatar nan ma an kashe mutane takwas a arewacin kasar. Duk da shirin tsagaita wuta, an ji ka rar ta shin bindigogi a birnin Damascus.

Karin bayani