Bom ya tawarwatse a garin Deraa na Syria

bom Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Bam ya fashe a Homs

Wani Bom ya tawarwatse a gefen titi kusada ayarin motocin masu sa ido na majalisar dinkin duniya akan tsagaita bude wuta a Syria, lokacin da suka ziyarci garin Dera'a dake kudancin kasar.

Sojojin Syria shida ne suka samu raunuka sakamakon tashin bam fashewar din.

Shugaban tawagar ta majalisar dinkin duniya, Manjo Janar Robert Mood dan kasar Norway na cikin ayarin motocin lokacin da Bom din ya fashe, amma bai samu ko kwarzane ba.

Can kuma a birnin Homs, wakilin BBC ya bada labarin cewar har yanzu ana cigaba da musayar wuta a birnin, tsakanin dakarun gwamnati dana 'yan adawa.

Wakilin BBC ya kara da cewar a yanzu haka an kauracewa unguwanni da dama na birnin Homs din sakamakon luguden wutar.

Karin bayani