Za'a gudanar da zaben majalisu a Algeria

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zabe a Algeria

A kasar Algeria za a gudanar da zabukan majalisar dokoki wanda gwamnatin da sojoji ke mara wa baya ta ce za'ayi adalci a cikinsa.

Gwamnatin ta bayyana cewar zaben shi ne mafi adalci da aka taba yi cikin shekaru da dama da suka wuce.

Akwai sababbin jam'iyyu da za su shiga wannan zabe amma yawancin 'yan takarar ko dai suna da alaka ne da jam'iyyar National Liberation Front mai jan ragamar gwamnati ko kuma suna da wata hulda ta kut-da-kut da gwamnatin.

Tashe-tashen hankulan siyasar da aka yi bara a kasashe da dama na Afrika ta arewa dai ba su shafi kasar ta Algeria ba.

Karin bayani