Obama ya goyi bayan auren jinsi guda

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Obama

Barrack Obama ya zamo shugaban farko na Amurka da ya goyi bayan aure tsakanin mutane masu jinsi daya.

A wata hira ta talabijin na ABC Mr Obama ya ce, shi da ma can yana nan kan bakan sa cewar lallai ne a yi ma Amurkawa 'yan luwadi da Madigo adalci a dauke su a matsayi daya daidai da kowa.

Sai dai Shugaban Amurkar ya ce ya shiga wani hali na rashin tabbas kan batun, wanda yanzu haka ya raba kan Amurkawa.

Lokacin da suke tofa albarkacin bakin su, Amurkawa sun bayyana ra'ayoyi mabambanta a kan kalaman na Mr Obama.

Wasu dai dama masu marawa Obaman baya Amurkawa yan asalin Afrika ba su ji dadin tunanin nasa ba.

Shi kuwa wanda za su iya gwamzawa da Obaman a zaben watan Nuwamba Mitt Romney ya ce yana kan bakansa na kin amincewa da auren jinsi daya.

Karin bayani