Ma'aikatan Birtaniya na shirin yajin aiki

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption David Cameron

Dubban ma'aikatan gwamnati a Britaniya na shirin tsunduma yajin aiki a yau don nuna adawar su ga sauye-sauyen da za a aiwatar a kan kudaden albashi da na fansho.

Ma'aikatan gwamnati da na dakunan ajiyar kayan tarihi da ma'aikatan lafiya suna cikin ma'aikatan da ake tsammani za su yi wani jerin-gwano, su ra tsa tsakiyar birnin London.

Gwamnatin kasar ta ce, ya zama wajibi a aiwatar da wadannan sauye-sauye a kan wasu ma'aikatan tare da zaftare kudaden fanshon don rage kudaden da gwamnatin ke kashewa.

Sai dai duk da wannan zanga-zanga, akwai alamun gwamnatin za ta aiwatar da wadannan sauye-sauye.

Karin bayani