Filato: an hallaka mutane bakwai

Rahotanni dake fitowa daga jihar Filato a Nijeriya na cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari a wani kauye dake karamar hukumar Riyom inda suka kashe mutane bakwai 'yan gida daya.

Rundunar 'yan-sandan jihar Filato ta ce a daren jiya ne aka kai harin, wanda kawo yanzu ba'a san ko suwaye suka kai shi ba, amma dai sun ce suna ci gaba da gudanar da bincike.

Karamar hukumar ta Riyom dai na daya daga cikin yankunan da tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci da addini, da kuma siyasa suka fi muni a jihar ta Filato inda a cikin 'yan shekarun nan dubban mutane suka rasa rayukansu.