Makarantar Sojin Amurka na kwas din kyamar Islama

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption General Dempsey

Wani babban hafsan sojoji a Amurka ya soki wani kwas da ake koyarwa a wata babbar makarantar sojoji a Amurka kan addinin Islama.

Wannan kwas da aka dakatar da koyar dashi a daya daga cikin manyan makarantun sojin kasar na koyar da sojin cewa babu wani sassaucin raayi a addinin Islama saboda haka su dauka addinin makiyin sune.

Koyarwar wannan kwas din yana nuni da yaki ta ko wacce fuska ga duk duniyar musulmai har ma da yiwuwar kai harin nuclea ga manyan birane na Makka da Medina da kuma kashe fararen hula.

Shugaban rukunin hafsan hafsoshin sojin Amurka Martin Dempsey ya soki lamirin koyarda kwas din yana cewa abunda ake koyar da manyan sojin da shi za suyi amanna.

General Dempsey, ya umarci a gudanar da bincike kan lamarin.

Karin bayani