Ana neman kafa sabuwar gwamnati a Girka

Zabe a kasar Girka Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zabe a kasar Girka

Shugaban jam'iyyar 'yan gurguzu a kasar Girka, Evangelos Venizelos ya ce ya kasa kafa gwamnatin hadin gwuiwa.

Ya ce zai mayarwa da shugaban kasar ikon kafa gwamnatin, wanda ake saran zai kira taro ran asabar game da kafa wata gwamnatin gaggauwa.

Wakilin BBC a Athens ya ce makomar Girka a kungiyar kasashen Turai dake amfani da kudin Euro ya sake shi ga wani hali rashin tabbas.

Kasar Jamus ta ce Girka baza ta sake samun bashi daga kasashen waje ba, muddin gwamnatin da za'a kafa ta ki amincewa da matakan tsuke bakin aljihun kungiyar.

Karin bayani