'Yan takara biyu sunyi mahawara a Masar

Hakkin mallakar hoto
Image caption Pasta a Masar

Miliyoyin 'yan kasar Masar sun kalli muhawarar farko ta talabijin kai-tsaye da aka yi tsakanin 'yan takarar Shugabancin kasar.

Mutane biyu dake sahun gaba da tsohon Shugaban kungiyar hadin kan larabawa Amr Moussa da Abdul-Moneim Abul-Fotouh mai matsakaicin ra'ayin kishin Islama sun kara da juna.

Mr Moussa ya soki lamirin abokin hamayyarsa a matsayin tsohon jagora a kungiyar nan mai karfi ta Muslim Brotherhood, yayinda Abul Fotoh din ya kira Amr Moussa tsohon Ministan harkokin waje na tsohuwar gwamnatin kama karya.

Sai dai a mahawarar ba wanda akayiwa cikakkiyar mahangurba.

Karin bayani