Najeriya: an kai hare-hare

A cigaba da samun asarar rayuka da ake fuskanta a Nijeriya sakamakon tabarbarewar sha'anin tsaro, a jiya da dare wasu yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, sun kashe mutane biyu ciki har da wani basaraken gargajiya, da kuma jikkata wasu mutanen biyu a jihar Bauchi.

Lamarin dai ya faru ne a wani kauye da ake kira Kutaru, dake yankin Tafawa Balewa mai yawan fama da tashe-tashen hankula, inda maharan suka tsere bayan aikata kisan.

A jihar Taraba ma na cewa, wani mutum akan babur ya jefa bam a kusa da wani banki a unguwar Dorawa dake cikin birnin.