An ci tarar kamfanonin salula a Najeriya

Goodluck Jonathan
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Kamfanonin wayoyin sadarwa na Najeriya guda hudu za su biya tarar Naira biliyan daya da miliyan dari da saba'in saboda rashin kyawun layukansu a watannin Maris da Afrilu na bana.

A cewar Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), tuni aka sanar da kamfanonin cewa za su biya wadannan kuadade na tara kamar haka: MTN da Etisalat za su biya Naira miliyan dari uku da sittin ko wannensu, yayinda kamfanin Airtel zai biya Naira miliyan dari biyu da saba'in; shi kuwa kamfanin Globacom Naira miliyan dari da tamanin zai biya.

Bugu da kari, wajibi ne kamfanonin su biya tarar nan da ranar 21 ga watan Mayu ko kuma su fuskanci tarar karin Naira miliyan biyu da dubu dari biyar a kan ko wacce rana guda da suka kara ba su biya ba.

Hukumar ta NCC ta ce wannan tara horo ce ga kamfanonin saboda saba Dokokin Tabbatar da Ingantuwar Aiki, ta hanyar gaza samar da mafi kankantar kyawun layukansu na waya.

A wasikar da ta aikewa kamfanonin, mai dauke da sa-hannun Daraktar Shari'a da Ingantuwar Aiki, Josephine Amuwa, da kuma Daraktan Sa-ido da Tabbatar da bin Doka, Ubale Maska, Hukumar ta ce ta lura cewa a watannin Janairu da Fabrairu ma kyawun layukan bai kai yadda aka kayyade ba, amma ta yanke shawarar ta dagawa kamfanonin kafa.