BBC navigation

Koyar da sojojin Amurka yaki da Musulunci?

An sabunta: 11 ga Mayu, 2012 - An wallafa a 09:36 GMT
Janar Martin Dempsey

Hafsan Hafsoshin Dakarun Amurka, Janar Martin Dempsey

Hasfan sojin Amurka mafi girma ya yi Allah-wadai da wani kwas da ake karantarwa a kan Musulunci a daya daga cikin manyan makarantun sojin Amurka, yana mai cewa "abin kyama" ne.

Wannan lamari dai ba abin mamaki ba ne. Labarin karantar da kwas din, wanda shafin intanet na Wired ya fara yadawa, yana da daure kai, kuma ba makawa ya fusata Hafsan Hafsoshin Rundunonin Tsaro, Janar Martin Dempsey.

Kwas din dai na karantar da jami'an soji ne cewa babu wani abu mai kama da matsakaicin ra'ayin addinin Musulunci, sannan kuma yana bukatarsu da su dauki Musulunci a matsayin abokin gaba.

Kwas din ya nemi a yaki Musulmin duniya ta ko wacce fuska, ciki har da, mai yiwuwa, kai hari da makaman nukiliya a kan biranen Makkah da Madina da ma shafe fararen hula daga doron kasa.

Ma'aikatar Tsaro ta Pentagon ta tabbatar da cewa kayan karatun kwas din da aka samu a shafinta na intanet gaskiya ne.

Wani abu bambarakwai

A gani na ba da nufin wasa-kwakwalwa a kan wuce-gona-da-iri da wadansu ka iya yi aka kirikiri wannan kwas din ba. Kwas din ya kunshi hakikanin abin da malamin da ke karantar da shi ya yi imani da shi.

Saboda haka ba abin mamaki ba ne da Janar Dempsey ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike a kan abubuwan da sauran makarantun soji ke karantarwa a kan Musulunci.

Ana dai karantar da kwas din ne ga manyan jami'an soji masu sha'awarsa a Kwalejin Horar da Manyan Sojoji da ke Norfolk a Jihar Virginia har tsawon shekara guda.

Janar Dempsey ya kwatanta kwas din da cewa ya yi "hannun-riga da dabi'unmu na mutunta 'yancin addini da al'adu" sannan kuma "abin kyama ne da rashin sanin ya kamata a ilmance".

Wannan al'amari dai ya bayyana ne bayan daya daga cikin jami'an da ke daukar darasin ya yi korafi a watan jiya.

Yanzu haka dai an kaddamar da bincike a kan yadda ma tun farko aka amince da kwas din da ma dalilin da ya sa har aka sanya shi a cikin manhajar karatun kwalejin.

Tuni dai aka dakatar da wani laftanar kanar daga karantarwa, amma kuma yana ci gaba da rike mukaminsa na soji—Pentagon na fatan samun cikkaken rahoto nan da karshen wannan watan.

Abin mamaki shi ne cewa dukkan kwamandoji, da kyaftin-kyaftin, da kanar-kanar din da suka dauki darasin ba su ji cewa ya kamata su sanar da kowa cewa ga wani abu bambarakwai yana faruwa ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.