An kashe jami'in gwamnatin Afghanistan

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban Afghanistan, Hamid Karzai

Rahotanni daga Afghanistan na cewa an kashe wani babban jami'i a Kwamitin Zaman Lafiya na gwamnatin kasar.

Kakakin rundunar 'yan sandan birnin Kabul, Mohammad Zahir, ya ce an kashe Arsala Rahmani ne akan hanyarsa ta zuwa wajen aiki.

Mr Rahmani, tsohon jami'in mayakan Taliban ne da ya koma mai shiga tsakanin gwamnati da 'yan kungiyar domin samun zaman lafiya.

A bara ne dai aka kashe tsohon shugaban kwamitin, Burhanuddin Rabbani.

Karin bayani