An yi harbe-harbe a Najeriya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan sandan Najeriya

Rahotanni daga garin Misau da ke jihar Bauchi a arewacin Najeriya na cewa an yi harbe-harbe da bindigogi da kuma jin karar fashewar abubuwa a ranar Juma'a.

Ganau sun ce an shafe fiye da sa'oi biyu ana jin harbe-harben, sai dai kakakin rundunar 'yan sanda ta jihar Bauchi, Muhammad Hasssan, ya shaidawa BBC cewa basu samu cikakken bayani game da lamarin ba.

A wani bangaren kuma rahotanni na cewa 'yan bindiga sun kashe wasu mutane a jihohin Kaduna da Gombe.

A jihar Gombe, 'yan binda sun hallaka wani mutum mai suna Baba Alhaji a garin Gombe.

A Kaduna ma, rahotanni sun ce an kashe wani basaraken gargajiya da kuma dan sanda a yankin Rigasa na jihar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Aminu Lawal, ya tabbatar da mutuwar dan sandan, sai dai ya ce ba su da labarin kisan basaraken gargajiyar.

Karin bayani