Ana gangami a Spain

Wata zanga-zanga a Spain Hakkin mallakar hoto AFP

Dubban jama'a ne a kasar Spain suka shiga wani jerin gwano domin cika shekara guda da wata zanga zanga da aka gudanar domin nuna adawa da matakan tsuke -bakin aljihu.

Ga abin da daya daga cikin wadanda suka shirya gangamin Ana Poncovo take cewa, 'mun hallara ne a nan yau domin cika shekara guda da kafa kungiyar sha biyar ga watan Mayu. Mun yi nasarar cinma wasu bukatu, amma ba su taka kara suka karya ba."

Akwai kuma wasu jerin zanga zangar da kungiyar Occupy ke jagorantar gudanarwa a birane da dama na duniya, ciki har da London.

Dubban 'yan kasar Spain ne suka shiga zanga zangar a bara, kuma tun daga lokacin matsalar tattalin arzikin kasar ta Spain na ta kara kamari.