Chavez ya koma Venezuela bayan an yi masa tiyata

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hugo Chavez

Shugaban kasar Venezuela Hugo Chavez ya koma kasar kwanaki goma sha daya bayan ya je Cuba inda ake yi masa maganin cutar sankara da ya ke fama da ita.

Ya bayyana ta gidan talabijin na kasar inda ya ce an kammala maganin da ake yi masa cikin nasara kuma yanzu a shirye ya ke ya sake tsayawa takara a zaben da za a gudanar a watan Oktoba.

Mr Chavez ya jima yana kai kawo tsakanin kasar sa da Havana tun da aka yi masa tiyatar ciwon sankara karo na biyu a watan Fabarairu.

Ya bayyana mutanen da ke yada jita-jitar cewa ciwon nasa ba na tahi ba ne, da cewa makiyan kasar ne, kuma ba za su yi nasara ba.

Zargin kisa

Mr Chavez ya koma kasar Venezuela ne a daidai lokacin da hukumar leken asirin kasar ta kama wani mutum da ke wallafa wasan hada kalmomi a wata jaridar kasar, inda ta ke zarginsa da rubuta wasu sakonni da a fakaice ke tunzura jama'a don su kashe wani kanen shugaba Chavez mai suna Aden.

Shi dai Neptali Segovia ya musanta aikata ba daidai ba.

Yanayin siysar kasar ta Venezuela dai sai dada dumama ya ke yi gabanin zaben da za a gudanar a watan Oktoba, inda bangaren shugaban kasar da na 'yan adawa ke zargin juna da yunkurin tayar da zaune tsaye.

Karin bayani