Ana zanga-zanga a kasashen Turai

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu zanga-zanga a Spain

'Yan sanda a Madrid babban birnin Spain suna korar daruruwan masu zanga-zangar da suka taru a dandalin Pueta dal Sol don bijirewa matakin tsuke-bakin-aljihun gwamnati.

Masu zanga-zangar, karkashin kungiyar nan ta Occupy the World, sun yi machi a birane irinsu Barcelona, da Madrid, da Moscow, da New York, da Athens, da London da kuma Frankfurt, inda suka yi Alla-wadai da kasuwannin kudi kan yadda suke gudanar da huldodinsu, wadanda a cewarsu suka fifita masu hannu-da-shuni.

An yi gangami da bore a garuruwa da birane kusan 80 da ke fadin kasar Spain.

Masu zanga-zangar sun ce mummunan halin tattalin arzikin kasar ne ke yi musu kaimi don su ci gaba da boren.

Sauran biranen Turai

Akasarin mutanen da ke gudanar da wannan gangami matasa ne da 'yan fansho da kuma iyalan da suke cikin matsanancin matsin tattalin arziki.

Alkaluma dai sun nuna cewa rashin aikin yi ya zarce kashi 24 cikin dari a Spain lamarin da ya sanya tattalin arzikin kasar ke ci gaba da fuskantar koma-baya.

Ana ci gaba da irin wannan zanga-zanga a wasu biranen na kasashe daban-daban wadanda suka hada da London da Lisbon.

Ines Subtil na daga cikin wadanda ke zanga-zangar a Lisbon, babban birnin kasar Portugal.

Ta ce suna gadanar da zanga-zangar ce domin bijirewa matakan tsuke-bakin aljihun gwamnati:

''Da fari, muna son yin zanga-zanga ce don kin amincewa da shirin tsuke-bakin-aljihu da kuma rashin aiki yi musamman a Portugal; mutane na cikin matsanancin hali''.

A Italiya, wadansu mutane ne suka kai hari kan ofishin Hukumar da ke Karbar Haraji don nuna fushinsu kan manufofin tsuke-bakin aljihun gwamnati.

A birnin London, 'yan sanda sun kama mutanen da suka yi jerin-gwano akan hanyarsu ta zuwa babban bankin kasar don gudanar da zanga-zanga.

Karin bayani