Afghanistan: an kashe Arsala Rahmani

Marigayi Arsala Rahmani Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Wani dan bindiga a Kabul, babban birnin Afghanistan ya kashe wani babban mai shiga tsakani, Arsala Rahmani. A da tsohon jami'i ne na kungiyar Taliban, kafin daga bisani ya kasance na gaba gaba da suka shiga shirin samar da zaman lafiya.

Kwamandan 'yan sanda, Janar Daud Amin ya ba da bayani game kisan Arsala Rahmani, yana cewa wani dan bindiga ne da ba a shaida ba ya harbe shi, ta hanyar amfani da bindiga mai salansa.

Manyan jami'an Afghanistan sun bayyana mutuwar Arsala Rahmani a matsayin babban koma-baya a shawarwarin sulhu da Taliban, suna cewa Shugaban Afghanistan ya dogara gare shi wajen fahimtar tunanin Taliban.