Serena ta lashe gasar Madrid bayan ta doke Azarenka

Hakkin mallakar hoto Reuters

Serena Williams ta nuna cewa har yanzu akwai jini a jika bayan da ta doke Victoria Azarenka a wasan karshe a gasar Madrid Open a ranar Lahadi.

Serena ta fidda Victoria Azarenka wadda itace ta daya a fagen Tennis din mata a duniya a wasanni biyu da maki 6-1 da kuma 6-3.

Serena mai shekarun haihuwa 30 kuma na tara a fagen Tennis din Mata ta fara ne da lallasa Azerenka da ci hudu da nema a wasan farko.