Ecowas za ta tura sojoji zuwa Guinea Bissau

 Ecowas za ta tura sojoji zuwa Guinea Bissau Hakkin mallakar hoto
Image caption Ecowas ta sha alwashin mayar da Guinea Bissau da Mali tafarkin demokuradiyya

Kungiyar raya tattalalin arzikin kasashen Afrika ta yamma, Ecowasta ce za ta tura sojoji fiye da dari daya zuwa kasar Guinea Bissau.

Kungiyar ta kuma ce tana san tura sojoji kasar Mali, amma ta ce har sai ta samu amincewar gwamnatin Mali kafin ta tura sojojin.

Wani taro da manyan hafsoshin tsaron kasashen kungiyar suka yi a Abuja, babban birnin Najeriya ne ya amince da matakin.

Kasashen na Mali da Guinea Bissau dai sun fuskanci juyin mulkin soji a baya-bayan nan kuma kungiyar Ecowas ta ce ta dau aniyar tabbatar da maido da su kan turbar demokuradiyya.

Ministan tsaron Najeriya Dr Bello Halliru, ya ce kasar za ta taimaka a duk wani shiri na samar da zaman lafiya.

Sai dai ya kara da cewa ba za su tura dakarunsu su yi zaman dirshen a wata kasa ba.

A ranar 22 ga watan Maris ne dai sojoji suka hamabarar da gwamnatin Mali sai dai daga bisani kuma sun mika mulki ga sabon mukaddashin shugaban kasa.

Haka kuma a ranar 3 ga watan Mayu ne sojiji suka hambarar da gwamnatin Guinea Bissau.

Karin bayani