Manyan jami'an bankin JP Morgan za su ajiye aiki

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tambarin JP Morgan

Rahotanni na cewa manyan jami'an bankin JP Morgan Chase na Amurka za su ajiye mukamansu bayan da bankin ya tafka asara ta dala biliyan biyu lokacin da ya yi wata hada-hadar kasuwanci mai cike da hatsari.

Jami'an su ne Misis Ina Drew, shugabar Sashen Zuba Jari da kuma shugabannin reshen bankin da ke London su biyu.

Rahotanni na cewa Misis Drew ta shaidawa masu hulda da bankin cewa ya kamata su zuba jarin da zai sanya bankin ya tsira daga matsalolin tabarbarewar tattalin arzikin da kasashen Turai suka fada a ciki, sai dai bayan da suka sanya jarin ne aka samu gagarumar matsala.

A ranar Alhamis ne dai shugaban bankin JP Morgan, Jamie Dimon, ya bayyana cewa bankin ya tafka asara wadda ya dora alhakinta akan wasu kura-kurai da daukar matakan da ba su dace ba.

Wannan lamari wani abin kunya ne ga bankin wanda ya yi ta ikirarin kasancewa na gaba-gaba a bin ka'idojin aikin banki musamman lokacin da aka fuskanci tabarbarewar tattalin arzikin duniya.

Hannayen jarin bankin sun fadi kasa warwar a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta New York a ranar Juma'a.

Karin bayani