Ina Drew ta yi murabis daga JP Morgan

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tambarin JP Morgan

Bankin JPMorgan ya ce babbar shugabar bangaren zuba jarinsa ta yi murabis bayan da bankin ya tafka asarar dala biliyan biyu lokacin da ya yi wata hada-hadar kasuwanci mai cike da hatsari.

Bankin ya ce Ina Drew, wacce ke sa ido kan harkokin kamfanin a London - inda aka tafka asarar, ta bar mukaminta ne bayan shafe shekaru 30.

Matt Zames, wanda ke rike da mukamin shugabancin hadin gwiwa a sashin zuba jari na bankin, zai maye gurbin Ms Drew.

A ranar Lahadi ne shugaban bankin JP Morgan, Jamie Dimon, ya bayyana cewa bankin ya tafka asara wadda ya dora alhakinta akan wasu kura-kurai da daukar matakan da ba su dace ba.

Wannan lamari wani abin kunya ne ga bankin wanda ya yi ta ikirarin kasancewa na gaba-gaba a bin ka'idojin aikin banki musamman lokacin da aka fuskanci tabarbarewar tattalin arzikin duniya.

Hannayen jarin bankin sun fadi kasa warwar da kashi goma cikin dari a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta New York a ranar Juma'a.

Yayin da a ranar Litinin suka fadi da kashi 3 cikin dari bayan bude hada-hada a kasuwar.

Karin bayani