Hollande zai sha rantsuwar kama aiki

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Francois Hollande

A ranar Talata ce sabon shugaban Faransa, Francois Hollande, zai sha rantsuwar kama aiki, lamarin da zai sanya ya zama shugaban kasa a karkashin jam'iyar 'yan gurguzu na farko da zai shiga fadar shugaban kasar cikin shekaru goma sha bakwai.

Da an rantsar da shi zai nada sabon Firayim Minista; kuma masana na ganin Jean-Marc Ayrault, shugaban 'yan jam'iyar gurguzu da ke Majalisar Dokoki ne ke kan gaba a jerin wadanda ka iya zama Firayim Ministan.

Daga nan ne kuma Mista Hollande zai fice zuwa Jamus, inda zai tattauna da shugabar gwamnatin kasar, Angela Merkel, game da tattalin arzikin Tarayyar Turai.

Misis Merkel, wacce ta goyi bayan shugaban Faransan da ya sha kaye a zaben da aka gudanar, Nicholas Sarkozy, ta dage cewa shirin tsuke-bakin-aljihun gwamnati da Tarayyar Turai ke amfani da shi shi ne zai fitar da kasashen daga kangin tattalin arzikin da suke ciki.

Sai dai Mista Hollande ya ce gwamnatinsa za ta fi bayar da muhimmanci ne ga bunkasar tattalin arziki da samar da ayyukan yi.

Karin bayani