PDP ta zargi Buhari da kokarin tunzura jama'a

buhari Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Janar Muhammadu Buhari na CPC

A Najeriya Jami'iyar PDP mai mulkin kasar ta zargi dan takarar shugaban kasa a zaben shekara ta 2011 na jam'iyar CPC, Janar Muhammadu Buhari da yin wasu kalaman da zasu haddasa tada zaune tsaye da zubda jini a kasar.

Wannan kuwa ya biyo bayan buga wata hira da wasu jaridun Najeriyar suka yi, inda suka ambato Janar Muhammadu Buharin na hasashen cewar zaben shekara ta 2015 zai kasance cikin mummunan zubda jini idan har ba ayi adalci ba.

A nata bangaran, jam'iyar CPC ta ce wani bita da kulli ne da jam'iyar ta PDP ke yiwa shugbanninta tun kafin zaben na 2015.

Bayan gudanar da zabukan shekara ta 2011, an samu tashe tashen hankula a wasu sassan Najeriya abinda ya janyo hasarar rayuka da dama.

Kuma a wancan lokacin gwamnatin Najeriya ta zargi 'yan adawa da hannu wajen jawo tashin hankalin, amma su 'yan adawa sun musanta hakan.

Karin bayani