Trao kan batun kare muhalli a Najeriya

Yadda masana'antu ke gurbata muhalli Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yadda masana'antu ke gurbata muhalli

A Najeriya, yau ne wata Kungiyar kula da muhalli mai zaman kanta ''Heinrich Böll Foundation'' ta gudanar da taron tattaunawa na masu ruwa da tsaki kan harkar muhallin.

Makasudin taron shi ne kaddamar da wani bincike kan yadda za a shawo kan matsalolin gurbatar muhalli, da ma yunkurin ganin yadda Najeriya za ta sauya daga dogaro kan kudaden shigar da take samu daga albarkatun man petur kawai, zuwa makamashin da ba ya gurbata muhallin.

Wannan al'ammari dai na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriyar ke shirin halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya a kan cigaba mai dorewa da za a yi a cikin watan Yuni mai zuwa a birnin Rio de Janeiro na Brazil.