Bikin Auren zawarawa dari a Kano, Najeriya

Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero (a gefen dama) da Sakataren Gwamnati Alhaji Rabiu Sulaiman Bichi
Image caption Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ne ya jagoranci auren tare da Sakataren Gwamnati Rabiu Sulaiman Bichi

Gwamnatin Jihar Kano a arewacin Najeriya ta mika kayan daki da gudunmuwar Naira dubu ashirin ga amare dari wadanda aka aurar a birnin Kano.

Gwamnatin ta mikawa amaren da angwayensu takardar shaidar aure a wani taro da aka gudanar a fadar gwamnatin.

Ranar Talata 15 ga watan Mayu ne dai aka daura auren matan su dari, akasarinsu zawarawa, da mazajensu.

Bikin na ranar Talata wani bangare ne na yunkurin Hukumar Hizba ta Jihar na aurar da zawarawa dubu daya a Jihar ta Kano.

Image caption Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso yana baiwa daya daga cikin amaren takardar shaida

Ko da yake akasarin wadanda aka aurar zawarawa ne, akwai wadansu maza da mata wadanda auren na ranar Talata na fari ne a wurinsu, kamar yadda wadansu daga cikin matan suka shaidawa BBC.

"Ba zawarawa kadai aka aurar ba, har da 'yanmata.... Za mu kai biyar ko shida a cikinsu", in ji wata amarya da ke auren farko.

Daya daga cikin wadannan ''yanmata' ta bayyana cewa saboda tana kaunar angon nata ta zabi shiga cikin zawarawan da za a aurar don ita ma ta ci gajiyar shirin na Hukumar Hisba.

Daya daga cikin zawarawan kuwa cewa ta yi tana matukar farin ciki. Da aka tambaye ta yadda zamanta a wannan auren zai bambanta da na baya sai ta kalli angon ta yi murmushi, sannan ta ce: "To, ina fatan dai zai rike ni amana".

Shi kuwa angon da aka tunkare shi da cewa ana zargin maza da cewa a farkon aure suke fara'a amma da an kwana biyu sai su fara daure fuska, sai ya ce: "to, nan dai ba za a samu haka ba, da izinin Allah".

Image caption Wasu daga cikin amaren yayin wata bita mako guda kafin daurin auren

Bayan daurin aure da bikin kuma, a cewar Malama Zahra'u Muhammad Umar, mataimakiyar kwamandan Hizba ta bangaren mata, akwai kuma walima.

"Za mu yi musu kwarya-kwaryar walima kamar yadda Musulunci ya tanada—ka san a Musulunce sai amarya ta shiga dakinta, wato sai bayan ta ga mijinta sannan ake walima", in ji Malama Zahra'u.

Image caption Akasarin wadanda aka daurawa auren zawarawa ne, ciki har da wannan dattijon, amma kuma akwai samari da 'yan mata

Ta kuma kara da cewa: "Mun yi tsare-tsare na bibiyar matsaloli—ba ma fatan matsala—amma ko wanne gida da ka sani [na wadannan ma'aurata] dari, da izinin Allah Hizba ta san da gidan, ta wayi ido da inda za a kai ko wacce amarya, kuma tana sane kunnenta na ji—in amarya ko ango ta/ya ce 'mhm' da izinin Allah Hizba za ta ji.

"Duk wanda ya sabawa wani Hizba za ta shiga domin sulhu, don dai a ci gaba da zaman lafiya".

Baya ga kayan daki da kuma jarin Naira dubu ashirin da gwamnatin Kano ta baiwa matan, Gwamnan Jihar, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce gwamnati za ta dauki nauyin kula da lafiyar ma'auratan.

Image caption Kadan daga cikin kayan dakin da aka baiwa amaren

"Wadanda duk aka samu da wata matsala, ko ta rashin lafiya, Allah gafarta Malam [Aminu Daurawa] a sanar da mu, za mu dauki nauyin kula da su", in ji Kwankwaso.

A lokacin da yake jawabi, Kwamanda Janar na Hukumar Hizba, Malam Aminu Daurawa, ya ce Hukumar ta tantace mata dubu hudu a yunkurin da ta fara na tantance yawan zawarawa.

Ranar Talata ne dai aka daura auren matan dari da mazajensu a karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Rabiu Sulaiman Bichi, a Babban Masallacin Juma'a na kusa da fadar Sarkin.

Karin bayani