Za'a fara shari'ar Mladic a Hague

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mladic

A yau ne za a fara sharia kan tsohon kwamandan sojojin Sabiyawan Bosnia Ratko Mladic.

Janar Mladic na fuskantar zargi 11 na laifukan yaki da suka hada da kisan kare dangi da halaka Musulmi dubu bakwai maza da yara kanana a Srebrenica a lokacin yakin Balkans na shekarun 1990.

Mladic yanzu ya kusa shekaru saba'in, shekaru sun cimmasa ga kuma rashin inganjin lafiya, shine kuma babban jami'i na karshe daga ya kin Balkans da zai fuskanci sharia a Hauge.

Ana tuhumarsa da kisan kare dangi da kuma laifuffuka na cin zarafi ga musulami Bosniyawa da Coshiyawa, gami da kashe musulmai manya da yara dubu bakwai a Srebrenica a shekarar alif da dari tara da casa'in da biyar.

Karin bayani