An biya masu ba da shaida a kaina —Taylor

Charles Taylor Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tsohon shugaban kasar Liberia, Charles Taylor, yayin da yake jawabi ga kotun duniya

Tsohon shugaban kasar Liberia, Charles Taylor, ya shaidawa kotun duniya dake Hague cewa masu shigar da kara sun biya masu bayar da shaida, ko sun tursasa su, su bayar da shaidar zur a kansa.

Mista Taylor, wanda aka samu da aikata laifuffukan yaki, ya fadi haka ne yayinda ya ke jawabin kare kansa, kafin a yanke masa hukunci nan gaba a wannan watan.

A cewarsa, shi mutum ne mai 'ya'ya, da jikoki, da tattaba-kunne, wanda ba ya barazana ga al'umma, don haka ya yi kira ga alkalai a Kotun Musamman mai Hukunta Laifuffukan da aka Aikata a Saliyo su bi hanyar yafewa-juna wajen yanke masa huknci ba ta ramuwar gayya ba.

Alkalan dai sun yanke hukuncin cewa tsohon shugaban na Liberia ya taimakawa 'yan tawaye masu dauke da makamai yayin yakin Saliyo, su kuma ['yan tawayen] sun saka masa da daimon din da aka hako ta hanyar bautatar da mutane.

Masu shigar da kara dai sun bukaci a yanke masa hukuncin zaman kaso na shekaru tamanin.

Karin bayani