Tallafin Birtaniya ya rage ingancin ilimi

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption David cameron

Birtaniya ta karbi wani rahoto wanda ya ce tallafin da Birtaniyar ke bayarwa don inganta ilmi a wasu kasashen Afirka, ya kai ga rage ingancin ilmin.

Wani bincike da wata hukuma mai zaman kanta ta gudanar, na nuna cewa an samu karin yara kimanin million 52 da suka shiga makaranta a kasashen Habasha da Rwanda da Tanzania a dalilin tallafin.

Sai dai abunda rahoton ya lura dashi shine karuwar yaran a makarantu ya sa an dauki karin malamai da ba su da kwarewa.

Gwamnatin Birtaniya ta ce, an maida hankali sosai kan adadin yaran da suke shiga makaranta, ba tare da laakari da ingancin ilmin ba.

Karin bayani