Kamfanin Facebook zai sayar da hannun jari

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Zuckerberg

Shafin internet na musayar ra'ayi na Facebook zai sayarda hannun jarinsa ga alumma ranar Juma'a a kan kowanne hannun jari dala talatin da takwas ($38).

Farashin ya sanya darajar Kamfanin ta kai dala biliyan dari da hudu. ($104b)

Wannan dai ita ce babbar kiman ta Kamfani da akayi na uku a tarihin Amurka.

A shekaru takwas da suka wuce tun lokacin da Shafin Facebook ya fara sada mutane ta hanyar sadarwar internet, an kidaya mutane miliyan dari tara ne ke amfani da shi a duniya baki daya.

Karin bayani