Bama bamai sun fashe a makarantu biyu a Kano

kano
Image caption Fashewar bama a Kano

A jihar Kano dake arewacin Najeriya kuma wasu boma bomai ne suka tashi a wasu makarantun firamare biyu.

Boma boman sun tashi ne jiya da daddare a makarantar firamare ta Ja'in dake Sharada da kuma sabuwar makarantar firamare ta Hotoron Fulani dake Hotoro a gabashin birnin na Kano.

Hukumomi sun ce babu wanda ya rasa ransa ko ya jikkata sakamakon hare haren, sai dai bayanai na cewa wasu motoci sun lalace sakamakon tashin bom din na makarantar ja'in.

Haka kuma wasu rahotannin na cewa an kashe wani mutum har lahira a unguwar rimin kebe yayin da aka jikkata wasu biyu a wani harin bindiga da aka kai musu jiya da daddare.

Karin bayani