Thabo Mbeki ya isa Sudan don yin sulhu

Hakkin mallakar hoto INTERNET
Image caption Thabo Mbeki

Tsohon shugaban Afrika ta kudu Thabo Mbeki ya isa kasar Sudan a matsayin mai shiga tsakanin Sudan da Sudan ta kudu, wanda Kungiyar tarayyar Afrka ta tura.

Fada dai ya sake barkewa ne watan da ya gabata tsakanin kasashen kan iyakar da suke takaddama akai.

Thabo Mbeki zai gana da shugaban kasar Sudan Omar el bashir da kuma wasu manyan jami'an kasar.

Iyakar dai na daya daga cikin abubuwan da ba a kai ga cimma daidaito akai ba lokacin da Sudan ta kudu ta samu cin gashin kanta watan Julin bara.

Majalisar dinkin duniya tayi barazanar kaka bawa kasashen takunkumi matsawar ba akai ga cimma daidato kan abubuwan da ake takaddama akai zuwa watanni uku ba.

Karin bayani