Chen Guancheng ya isa Amurka

Chen Guanchen
Image caption Chen Guanchen

Mai fafutukar nan dan China, Chen Guancheng, wanda ya sauka a Amurka tare da matarsa da 'ya'yansa biyu, ya yi godiya ga gwamnatin kasar ta Amurka.

Mista Chen ya ja hankalin jama'a a fadin duniya ne bayan ya tsere daga gidansa inda ake yi masa daurin talala a arewa maso gabashin China, ya kuma samu mafaka a ofishin jakadancin Amurka a Beijing.

Da yake jawabi a New York, Mista Chen ya kuma yaba wa China saboda yadda ya ce ta kai zuciya nesa.

"Bayan an yi ta fadi-tashi, a karshe dai na baro Shandong tare da taimakon abokaina. Ina matukar godiya ga ofishin jakadancin Amurka da ma gwamnatin China saboda alkawarin da ta yi na kare hakkoki na na dan kasa."

Sanye da bakin tabarau, yana kuma dogarawa da sandar guragu, mai fafutukar makaho mai shekaru arba'in, ya samu gagarumar tarba a wani ginin jami'a a kauyen Greenwich inda zai zauna a Amurka.

Da ya ke jawabi ga taron magoya bayansa da kuma 'yan jarida, Chen Guanchen ya mika godiyarsa ga kasar Amurka da ta ba shi mafaka a ofishin jakadancinta da ke Beijin.

Sai dai ya kuma yaba wa gwamnatin China ita ma saboda dattakon da ya ce ta nuna.

Wannan tattausan kalami a kan China na iya nuni ga damuwar da Mista Chen ke da ita dangane da makomar 'yan uwansa da ke China.

Matarsa da 'ya'yansa biyu ne kawai suka bi shi Amurka.

Kafin ya shiga sabon gidansa, mutumin da ya kangare wa gwamnatin China ya ce a yanzu yana bukatar ya huta.

Karin bayani