Mutane sun rasu a girgizar kasar Italiya

Girgizark kasar Italy Hakkin mallakar hoto Reuters

Wata girgizar kasar da ta afka wa arewacin kasar Italiya, ta yi sandiyar mutuwar mutane hudu, yayin da dubban mutane suka tsere daga cikin gine-gine zuwa kan tituna.

Girgizar kasar mai karfin 6.0 ta faru ne da tsakar dare, kimanin kilo mita 35 a arewacin birnin Bologna.

Jami'ai a kasar sun ce mutane hudun sun mutu ne a lokacin da ginin da suke aiki a ciki ya rufta musu.

Gidan talabijin na Italiya ya nuna masana'antun da suka ruguje.

Masu ceto na ci gaba da bincika baraguzan gine-gine yayinda rahotanni ke nuna cewa akwai mutane da dama da ke binne a cikinsu.

Rahotanni sun ce kimanin mutane 50 ne suka samu raunuka sakamakon girgizar kasar.

Karin bayani